Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Ko Mai Yasa Haka kuwa ...

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin kwace wayoyin salula guda 431 na dindindin tare da mika su ga Gwamnatin Tarayya, bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin kwace wayoyin salula guda 431 na dindindin tare da mika su ga Gwamnatin Tarayya, bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta bayyana cewa na’urorin na da alaka da ayyukan damfarar intanet.

Mai shari’a Deinde Dipeolu ne ya bayar da umarnin a ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026, bayan sauraron bukatar da EFCC ta gabatar ta hannun lauyarta, Hanatu Kofarnaisa.

A cewar EFCC, wayoyin na da alaka da wani cibiyar da ake kira “HK” a Victoria Island, Legas, inda ake zargin wasu ’yan kasashen waje da daukar matasan Najeriya da horas da su kan dabarun damfarar soyayya, zuba jari da harkokin cryptocurrency.

Takardun da EFCC ta gabatar wa kotu sun ce wani samame da hukumar ta kai ranar 10 ga Disamba, 2024, ya kai ga kama daruruwan mutane, ciki har da ’yan Najeriya da ’yan kasashen waje, musamman ’yan China da Filipinas. Hukumar ta ce wadanda ake zargin sun fi mayar da hankali kan mutane a Amurka, Canada, Mexico da wasu kasashen Turai.

Binciken ya kuma danganta kamfanin Genting International Company Limited (GICL) da Huang Haoyu, wanda ake kira Ken, da wasu bangarori na ayyukan da ake zargin an gudanar.

EFCC ta ce Huang da kamfanin sun fuskanci tuhuma da suka hada da laifukan intanet, safarar kudade da haramtattun hada-hadar kudaden kasashen waje, kuma daga baya suka amsa wasu tuhume-tuhumen da aka yi musu tare da samun hukunci a kotu.

Tun a ranar 8 ga Yuli, 2026, kotun ta bayar da umarnin rikon wayoyin na wucin gadi, tare da bai wa masu ikirarin mallakar su damar bayyana. EFCC ta ce ta wallafa sanarwar kotun a jaridar The Guardian ranar 11 ga Agusta, amma babu wanda ya gabatar da objection cikin wa’adin da aka bayar.

Bayan nazarin hujjojin da aka gabatar, kotun ta amince da bukatar EFCC tare da bayar da umarnin mika wayoyin guda 431 ga Gwamnatin Tarayya na dindindin.

More from TimesPosts