Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Technology. ::: Ko Kunsan Mai yasa manta Shugaban Kasashe ke Rufe camera 📸 Idan Sunje Wajan Taro

Shin ko kasan dalilin da yasa manyan shugabannin ƙasashe suke sanya Tef ko Sticker a Camera 📸 ɗin wayoyin su a lokacin da suka halarci manyan taron ƙasashen duniya?. Malam this life is beyond your…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Shin ko kasan dalilin da yasa manyan shugabannin ƙasashe suke sanya Tef ko Sticker a Camera 📸 ɗin wayoyin su a lokacin da suka halarci manyan taron ƙasashen duniya?. Malam this life is beyond your expectations. Akwai wani dalili mai ban tsoro da ya sa suke yin hakan bawai kawai tumɓele bane marar dalili. Babban matakin tsaro ne da ake amfani da shi saboda madatsa harkar na'ura na gani kashe Ni. Akwai waɗanda aikun su kenan dare da rena wajen Hacking ko neman duk wani bayanan sirrin wani mutum mai matuƙar muhimmanci a duniya. Mostly shugabanni suna sanya wannan tef ɗin ne a kan Camera na wayar su ne saboda akwai yiwuwar Hackers zasu iya kunna Camerar wayar ba tare da shi kansa mai wayar ya sani ba. Ga Shugaban Ƙasa ko Yariman wata Masarauta wannan wani abu ne mai matuƙar tayar da hankali.

Idan Hackers suka kutsa cikin wata waya guda ɗaya a lokacin wani taro na sirri, hakan na iya basu damar ganin duk wasu takardu da ke kan wannan table ɗin, zasu iya hango fuskokin duk mutanen da ke cikin ɗakin, zasu iya bin duk wani abu da aka rubuta a littafin rubutu, taswira ko Notepad ɗin wannan wayar, hakazalika kuma zasu iya sauraren ko gano duk wani wanda mai wayar yake magana dashi da kuma lokacin da suke yin wayar (kuma wlh ba za su taɓa ji ko ganin wata alamar cewa an kunna Camerar wayar ba). Da zarar sun yi Hacking Camerar wannan wayar, kai tsaye zasu iya kunna voice recording sannan su zare duk wani security Check-up dake kan wayar so that zasu compromising duk wata data da suke so a wannan wayar including shi kansa surrounding environment ɗin da wayar take. Ka je ka kalli Film ɗin Money Heist zaka gane me nake nufi.

Da irin wannan Hacking ɗin ne manyan Hackers da manyan hukumomin leƙen asiri suke gano duk wasu bayanan sirrin shugabanni a duniya. Shiyasa za kaga ko a taron Majalisar Ɗinkin Duniya manyan mutane irin su Donald Trump, Sheɗanyahoo, Mark Zuckerberg, Elon Musk, jami'an FBI, CIA da duk mutanen da suke da alaƙa da wani muhimmin Office ko aiki basa taɓa yarda Camerar wayar su ta zama a buɗe including Front Camera ɗin su. Duk wanda tsautsayi yasa Hackers ɗin nan suka cafki maƙwogoron Camerar wayar sa billahillazi ya kaɗe. Zasu naɗe duk wani muhimmin abu dake tattare da mutum ne including your voices, chat messages and even your future plans ba tare da mutum ya sani ba. Duk wani motsin ka kar suke kallon ka wlh. The worst part of ɗin shine ko rufe wayar kayi wlh sai sun kunna ta daga inda suke. Hackers jarabar duniya ne alaji. Abun ya wuce duk yadda kake tsammani ka ji. Kai dai kawai ka tsaya ka nemi na wake da shinkafa a Nigeria. Wannan layin sam ba irin layin ka bane Garzali Miko🙅🫂.

©Salisu Yakubu

More from TimesPosts