Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Kwamishinan ƴansanda na Kano ya bukaci Sarki Aminu Ado ya janye shirin sa na Hawan Fatahu Yakasai

Kwamishinan ƴansanda na Kano ya bukaci Sarki Aminu Ado ya janye shirin sa na Hawan Fatahu Yakasai Kwamishinan ƴansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Kwamishinan ƴansanda na Kano ya bukaci Sarki Aminu Ado ya janye shirin sa na Hawan Fatahu Yakasai

Kwamishinan ƴansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa yadda yake mutunta doka da kuma bin umarnin hukumomin tsaro.

Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban-girma da ya kai wa Sarkin a fadarsa da ke Nasarawa, Kano. Ziyarar ta biyo bayan sanarwar da Sarkin ya gabatar wa hukumomin tsaro na cewa zai yi tattaki a kan doki zuwa Yakassai domin halartar bikin saukar Alƙur’ani.

Kwamishinan ya ce manufar ziyarar ita ce roƙon Sarkin da ya dakatar da shirin hawan dokin, domin kare zaman lafiya da tsaron jama’a.

Ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun tanadi cewa duk wanda ke shirin gudanar da hawan doki ko wani taro, ya kamata ya sanar da su a rubuce aƙalla sa’o’i 72 kafin taron. Sai dai ya ce a wannan karon hukumomin sun fi son a soke hawan dokin gaba ɗaya.

Bakori ya roƙi Sarkin ya je wajen taron da mota kamar yadda ya saba yi, yana mai cewa hukumomin tsaro na son kauce wa duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali ko barazana ga zaman lafiyar Kano.

Kwamishinan ya kuma bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin basaraken da ke mutunta doka, wanda a kai a kai yake bin umarnin hukumomin tsaro tare da fifita zaman lafiya.

Ya roƙi Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, Sarkin Dawaki Babba, da wani babban mai ba Sarkin Kano shawara, da su ci gaba da mara wa Sarkin baya tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninsa da hukumomin tsaro.

Da yake mayar da martani, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya gode wa kwamishinan da tawagarsa bisa ziyarar, tare da tabbatar musu da cikakken haɗin kansa. Ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano na daga cikin abubuwan da ya fi bai wa muhimmanci, kuma zai ci gaba da goyon bayan duk wani ƙoƙari na tabbatar da doka da oda.

More from TimesPosts