Labaran chiki Gida Nigeria. :: Sarki Sanusi ya kai ziyara ga Olubadan a Ibadan don ƙarfafa alaƙar Hausawa da Yarabawa
Sarki Sanusi ya kai ziyara ga Olubadan a Ibadan don ƙarfafa alaƙar Hausawa da YarabawaMai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyara fadar Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, domin…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Sarki Sanusi ya kai ziyara ga Olubadan a Ibadan don ƙarfafa alaƙar Hausawa da Yarabawa
Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyara fadar Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, domin ƙarfafa dangantakar tarihi tsakanin Hausawa da Yarbawa.
Sarkin ya kai ziyarar ne ranar Lahadi a fadar Olubadan da ke Oke-Aremo, cikin birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, tare da rakiyar dimbin mabiyansa.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Sarkin ya bayyana farin cikinsa da sake ziyartar fadar, yana mai cewa ya dade yana da kyakkyawar alaƙa da al'ummar Ibadan tun kafin hawansa sarautar Kano.
“Babban farin ciki ne a gare ni na sake ziyartar fadar Olubadan. Na dade ina da kusanci da ’yan asalin Ibadan tun kafin na zama Sarkin Kano. Saboda haka, Ibadan tamkar gidana ne,” in ji shi.
Rahoton jaridar PUNCH ya ce sarakunan biyu sun fara gudanar da ganawar sirri a cikin fada kafin daga bisani su fito zuwa babban ɗakin taro domin yi wa sauran mahalarta jawabi.
Ziyarar na da nasaba da kyakkyawar alaƙa da dadadden zumuncin da ke tsakanin al'ummomin Hausawa da Yarbawa.
More from TimesPosts

Labaran Duniya. ::: IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂
IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana cewa hanya daya tilo da Amurka za ta iya cin nasara ga Iran ita ce kai mata farmakin sojojin kasa,…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya ::: Yau Shekaru 79 da Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga cikin manyan bindigogin kai hari na farko
Yau Shekaru 79 da Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga cikin manyan bindigogin kai hari na farkoA Ranar 13 Ga Watan Nuwamba 1947 Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga…
Ay Abdullahi3 min read

Labaran Duniya :: Kasar Saudiyya. Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure ba
Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure baWata kotun ƙasar Saudiyya ta yanke wa wata ƴar aikin gida 'yar Kenya mai shekaru 40, Esther Wanja…
Ay Abdullahi2 min read