Labaran Duniya. :: AN GANO SHI
AN GANO SHIRundinar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Zamfara, ta samu nasaran gano Matashin dan agaji na kungiyar Izala wanda yayi kalamai masu hatsari akan mabiya addinin Kirista a lokacin da suke…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

AN GANO SHI
Rundinar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Zamfara, ta samu nasaran gano Matashin dan agaji na kungiyar Izala wanda yayi kalamai masu hatsari akan mabiya addinin Kirista a lokacin da suke atisaye da yara kanana sanye da kakin 'yan agaji na kungiyar Izala
Matashin mai suna Umar Ibrahim Gandi Maradun, dan asalin karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, an haifeshi a ranar 15 ga Satumba, 2004, yanzu yana da shekaru 22
Binciken farko ya nuna cewa an dauki bidiyon ne a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba,2026, lokacin da Umar Ibrahim yana kan hanyarsa ta zuwa Masallacin Aliyu Ibn Abi Thalib, inda aka ce shi da wasu mutane suna bayar da tsaro a lokacin sallar Juma’a da wa’azi
Bayan bayyanar wannan bidiyo, rundunar 'yan sanda ta gaggauta tura jami’an leken asirinta domin gano mutanen da abin ya shafa da kuma tabbatar da halin da ya kai ga faruwar lamarin
Makarantun da aka gano suna da alaka da bidiyon su ne Nurul Islam Islamiyya da Akidatul Sahiha Islamiyya, wadanda dukkansu suke a karamar Hukumar Maradun, mai tazarar kusan kilomita 120 daga Gusau, babban birnin jihar Zamfara
Rundunar 'yan sanda ta tattauna da shugabannin JIBWIS a matakin Kasa da na jiha, daga bisani JIBWIS ta kama Matashin ta mika shi ga rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara domin gudanar da bincike
Umar Ibrahim ya halarci Makarantar Firamare ta Mualledi Model da ke Maradun, da kuma Government Day Secondary School, Maradun, ya shiga JIBWIS a shekarar 2025, sannan kwanan nan ya samu gurbin karatu domin yin digirin farko na Kimiyya a fannin Sadarwa da Yada Labarai (Mass Communication) a Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara
Rundunar 'yan sanda ta fara gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari, da zarar an kammala binciken, zata gurfanar da matashin a gaban kotu bisa zargin aikata laifuffukan da suka shafi tunzura mutane zuwa tashin hankali, tada hankalin jama’a da kuma barazanar aikata laifi
Sanarwa daga Kwamishinan 'yan sanda na jihar Zamfara CP A. M. Bello, PSC+, MNIPS, CCNP
Shikenan an rufe wanann babin, ita Izala bata karantar da tashin hankali balle tayi hari a kan wani, Matashin shekaransa guda da shiga kungiyar Izala, dama bai santa ba
Allah Ka kare mana kungiyar Izala daga sharrin masharranta
More from TimesPosts

Labaran Duniya :: Tsuntsu Mai wayyo...
Wannan Mata me Suna Aisha Ahmad Abdullahi yar asalin Jahar Niger State ce Amma tana Aure a Kaduna Road inka wuce Dutsen Zuba ta Kirki Wani kasuwanci ita da Mijinta Wanda sukai inviting na Mutane da…
Ay Abdullahi2 min read

Labaran Duniya ::: YAYI SHIRME SHIMA
YAYI SHIRME SHIMA.Kylian Mbappé ya fuskanci suka a China bayan da ya kira wani hoton barkwanci (meme) na Mao Zedong da ke nuna shi a matsayin wani azzalumin shugaban China.Real Madrid ta nemi a fuwa…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya. :: Rashin shakar iska ne ya yi ajalin masu haƙar ma’adinai 37 a hannun jami'an NSCDC - Kwamitin bincike
Rashin shakar iska ne ya yi ajalin masu haƙar ma’adinai 37 a hannun jami'an NSCDC - Kwamitin bincikeKwamitin bincike mai zaman kansa da Gwamnatin tarayya ta kafa ya gano cewa mutane 37 da ake zargin…
Ay Abdullahi1 min read