Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran Duniya. :: Rashin shakar iska ne ya yi ajalin masu haƙar ma’adinai 37 a hannun jami'an NSCDC - Kwamitin bincike

Rashin shakar iska ne ya yi ajalin masu haƙar ma’adinai 37 a hannun jami'an NSCDC - Kwamitin bincikeKwamitin bincike mai zaman kansa da Gwamnatin tarayya ta kafa ya gano cewa mutane 37 da ake zargin…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Rashin shakar iska ne ya yi ajalin masu haƙar ma’adinai 37 a hannun jami'an NSCDC - Kwamitin bincike

Kwamitin bincike mai zaman kansa da Gwamnatin tarayya ta kafa ya gano cewa mutane 37 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ne, sun mutu sakamakon rashin shaƙar iska a hannun jami’an hukumar tsaro ta NSCDC a Jihar Neja.

Shugaban kwamitin, Jonathan Kure, tsohon mataimakin darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin miƙa rahoton binciken ga ministan harkokin cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, a Abuja.

Rahoton ya nuna wani sabon mataki a binciken mutuwar mutanen 37, waɗanda suka rasu a ranar 17 ga Satumbar 2026, lokacin da suke tsare a hannun rundunar NSCDC ta Jihar Neja da ke Minna.

An kama waɗanda suka mutu ne tare da wasu mutane yayin samamen da jami’an tsaro suka gudanar kan masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a yankunan M.I. Wushishi da Lukoto na jihar.

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin ne domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar mutanen da kuma gano abubuwan da suka faru lokacin da suke tsare a hannun jami’an hukumar.

Sai dai, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da cikakkun bayanai kan sauran abubuwan da kwamitin ya gano ko shawarwarin da ya gabatar ba.

More from TimesPosts