Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran Duniya :: Tsuntsu Mai wayyo...

Wannan Mata me Suna Aisha Ahmad Abdullahi yar asalin Jahar Niger State ce Amma tana Aure a Kaduna Road inka wuce Dutsen Zuba ta Kirki Wani kasuwanci ita da Mijinta Wanda sukai inviting na Mutane da…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Wannan Mata me Suna Aisha Ahmad Abdullahi yar asalin Jahar Niger State ce Amma tana Aure a Kaduna Road inka wuce Dutsen Zuba ta Kirki Wani kasuwanci ita da Mijinta Wanda sukai inviting na Mutane da yawa suka Shiga wannan kasuwanci nasu yadda abin yake shine.

Suna yawo suna Gayawa Mutane Cewa idan ka saka 1,5m to Za'a na baka 250K duk Karshen Wata da Al'umma sukaji haka sai fa sukai ta Narka kudinsu a ciki inda ta Nunawa Mutane Cewa itafa ba Online business take ba Physical business ne domin kuwa daga cikin Abokan kasuwanci ta da take bawa kaya har Kamfani Yahuza suya inda tace duk wani Yahuza suya dake Nigeria tana basu kaji.

Wannan shine yasa Mutane suka kara yarda da ita sukai ta bata Kudadensu a juya musu ana basu riba Daga ciki harda wacce aka bata Kudin Kayan Auren kanwarta akan taje Ta siyo kayan ta dauki Kudin taba wannan Matar a juya a Basu riba Sanna Akwai Wata kuma tana da Babura data siya ta bayar ake Okada dasu ana bata Kudin ta Karbo Wa'enan Mashina ta siyar taba wannan Matar a Juya ana bata riba Every end of months.

Sannan Akwai Wata wacce Mijinta ya siya Mata Motor GLK itama tace tana bukatar ta Shiga wannan kasuwanci Bata son wannan GLK din saboda haka tace zata Siyar da GLK ta bayar ana juyawa ana bata riba sai ta Rinka tara Ribar daza ana bata inta tara sai ta siya Kalar motor da take so da Ribar Kudin Motor kuma suna nan, aikuwa daga jin haka sai ita wannan Matar me Juya Kudi tace zata siya Motor.

Sai me motor tace to ai shikenan tunda kina son motor ki dauketa muyi ciniki sai ki sakamin Kudin a Kasuwanci, to a Halin Yanzu dai an nemi Hajiya Aisha me Juya Kudi an rasa Sama da Kasa in an kirata a waya ba'a samunta ankai Kararta Wajen Jami'an Tsaro sun fara Tracking nata data Fahimci ana tracking dinta sai ta cire SIM din da aka santa dasu Yanzu babu halin Tracking.

Sannan Akwai Danta dake Zaune a Unguwar shima ya Gudu baya nan sannan anje an tambayi Yahuza suya da tace tana basu Kaza sunce suma basu santa ba kuma suma tunda tana karya da sunansu zasu nemeta Domin su Dauki Mataki akanta saboda haka Yanzu an saka Cigiya duk Wanda yaga ko yaji Labarin inda Aisha Ahmad Abdullahi take inya bayyana ta Yana da Wata Babbar Kyauta me Tsoka.

More from TimesPosts