Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran Duniya. Zanga-zangar ƴan bana-bakwai ta rikide zuwa rikici a manyan biranen Jamus

Zanga-zangar ƴan bana-bakwai ta rikide zuwa rikici a manyan biranen JamusZanga-zangar matasan Jamus ƴan bana-bakwai wato Gen Z ta rikide zuwa tarzoma da satar kayayyaki a wasu manyan biranen ƙasar,…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Zanga-zangar ƴan bana-bakwai ta rikide zuwa rikici a manyan biranen Jamus

Zanga-zangar matasan Jamus ƴan bana-bakwai wato Gen Z ta rikide zuwa tarzoma da satar kayayyaki a wasu manyan biranen ƙasar, bayan dubban matasa sun fito kan tituna domin nuna adawa da tsadar rayuwa da ƙarancin tallafin makarantu.

Zanga-zangar, wadda ƙungiyar Gen Z regelt ta shirya, ta gudana a fiye da birane 30, inda matasan suka kuma nuna adawa da rage kasafin kuɗin gwamnati da yiwuwar dawo da aikin soja na dole.

Rahotanni sun ce zanga-zangar ta kasance cikin lumana da rana, sai dai ta rikide zuwa rikici da daddare a biranen Frankfurt, Hamburg, Cologne da Leipzig, lamarin da ya tilasta wa jami'an tsaro amfani da ruwan da ke tarwatsa jama'a da barkonon tsohuwa.

A Frankfurt, wasu masu zanga-zangar da suka rufe fuskokinsu sun farfasa shaguna, tare da wawashe kayayyaki da jifan 'yan sanda da duwatsu da wasu abubuwan fashewa.

'Yansanda sun kama kusan mutane 30, yayin da wasu jami'ansu suka jikkata sakamakon arangama da masu zanga-zangar.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Lina Friedrich, ta ce matasan na fafutukar tabbatar da zaman lafiya da 'yanci maimakon yaƙi da tilastawa mutane shiga aikin soja.

Ta kuma bayyana cewa suna buƙatar inganta harkokin lafiya da ilimi tare da tabbatar da adalci wajen raba nauyin da ke kan al'umma.

Wannan zanga-zanga na zuwa ne bayan irin ta da matasa suka gudanar a Faransa, inda sama da mutum 320,000 suka fito zanga-zanga a ƙarshen mako na uku a jere.

More from TimesPosts

Labaran Duniya. Zanga-zangar ƴan bana-bakwai ta rikide zuwa rikici a manyan biranen Jamus | TimesPosts