Labarin mutuwar wani matashin soja da ake zargin jami'an NDLEA sun kashe shi abin tashin hankali ne.
Ya kamata a dauki mataki Labarin mutuwar wani matashin soja da ake zargin jami'an NDLEA sun kashe shi abin tashin hankali ne.Yadda masu rawaito labarin Ke bayyanawa dai wannan matashin soja yayi…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

Ya kamata a dauki mataki
Labarin mutuwar wani matashin soja da ake zargin jami'an NDLEA sun kashe shi abin tashin hankali ne.
Yadda masu rawaito labarin Ke bayyanawa dai wannan matashin soja yayi kokarin bayar da kariya ga wasu da ake zargi da hulda da miyagun kwayoyi har ta kai an sami sabani kuma jami'an sun sakarwa wannan soja darma.
Abin tashin hankali da ke bukatar mahukuntan rundunar soji da na NDLEA su tsoma baki shine, naga wani soja ya fara yin kira ga abokan marigayin kan su fito su daukar masa fansa, wanda nasan Karon ba zai kyau ba, yakamata a yi gaggawar daukar mataki domin a bayanin wannan matashi,shi marigayin ya fitar da wuka su kuma Jami'an NDLEA suka har be shi bayan sun same shi suka kara masa harbin suka kuma dauke shi suka tafi da shi ofishin su maimakon asibiti, kamar yadda wannan soja yace shaidun gani da ido sun rawaito.
Irin wannan idan har ya tabbata to gaskiya jami'an sun wuce makadi da rawa wajen karin yin harbi na 2 ,domin babban abin da aka fi so a doka shine kama mutum domin gurfanar da shi a gaban kotu dan haka harbin farko ya zama wajibi tun da ya fitar da wuka,amma harbi na 2 bidi'a ne a tsarin aiki yin hakan kuma tamkar daukar doka a hannu ne idan har hakan ya tabbata.
A takaice dai wannan lamari zai iya zama gagarumin rikici a tsakanin jami'an soji da na NDLEA wanda ka iya jawo batacciya ko kuma kare jini biri jini,dan haka ya zama wajibi a yi gaggawar shiga tsakani ayi wa tufkar hanci a kafa bincike a gurfanar da wadanda suka yi harbin idan sun yi laifi a hukunta su domin kaucewa barazanar da ka iya afkuwa idan har abokan aikin marigayin sun dauki shawarar wannan matashin dake kira da a daukar wa marigayin fansa.
Allah ya zuwa wutar ruwan sanyi ya kiyaye gaba.
More from TimesPosts

A KUNGYIYAR BOKO HARAM WANENE BAKURA BUDUMA, KUMA ME YA SA SUNANSA YAKE DA MUHIMMANCI?
A KUNGYIYAR BOKO HARAM WANENE BAKURA BUDUMA, KUMA ME YA SA SUNANSA YAKE DA MUHIMMANCI?Bakura Doro, wanda aka fi sani da Abu Umaima ko Abu Umayma, yana daga cikin sunayen da aka danganta da jagorancin…
Ay Abdullahi1 min read

Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan ’yan Bangladesh biyu bisa aikata lalata a cikin masallaci a Makka
Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan ’yan Bangladesh biyu bisa aikata lalata a cikin masallaci a MakkaMahukuntan Saudiyya sun sanar da kashe wasu ’yan ƙasar Bangladesh biyu bisa zargin aikata…
Ay Abdullahi1 min read

Kocin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta 1996 ya ce har yau bai karɓi lambar zinare ta lashe gasar Olympic ba bayan shekaru 30
Kocin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta 1996 ya ce har yau bai karɓi lambar zinare ta lashe gasar Olympic ba bayan shekaru 30Tsohon kocin Super Eagles, Jo Bonfrere, ya ce har yanzu bai karɓi lambar…
Ay Abdullahi1 min read