Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI

SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI Haihuwa ɗaukaka ce, bakuwa a samun daukaka sai anjure, iyayen mu nada shiri suke mata na gaske, shiyasa wata saita gama naƙuda ta haihu ɗaki daya ga mijinta yana Bacci…

Ay Abdullahi · Admin

· 3 min read

SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI

Haihuwa ɗaukaka ce, bakuwa a samun daukaka sai anjure, iyayen mu nada shiri suke mata na gaske, shiyasa wata saita gama naƙuda ta haihu ɗaki daya ga mijinta yana Bacci batare da ta tashesa, sai bayan ta haihu wata zata tashesa ko inyaji kukan jariri. Suna ganin abin kunya ne aji Mace na kuka ko ihu wajen naƙuda.

Toh amma a wannan lokacin bama kuka da ihun ba, matsayina na likita ina yawan samun tambaya akan wata sabuwar al'ada dake neman zama jiki, wadda ke matukar damu na saboda fargaba na irin hatsarin da take tattare dashi.

Mata da dama na zuwa suna tambaya ko ya dace suje ai musu allura ko basu maganin taso da naƙuda (induction)? domin kawai sun gaji da nauyin ciki, ciwon baya, kasala, ciwon jiki ko ciwon mara irin na ƴan kwanakin karshen ciki

Ina tausaya muku sosai. Mun sani kwanaki ko satukan karshe na ciki nada matuƙar wahala da gajiyarwa.... Amma tambayar da ya kamata kowace uwa ta yiwa kanta ita ce: Wanne irin iyaye muke son zama? Idan har ba zamu iya jure wahalar sati uku zuwa hudun ƙarshe na dakon amincin Allah ba, ta yaya zamu jure kalubale da dawainiyar shekaru masu yawa na tarbiyyar yaron?

Kurum saboda ciki ya kai sati 36 ko 37, sai ace lallai a tilasta wa jiki naƙuda? Wannan mataki ne mai cike da hatsari, kuma mara tushe da za'a iya kauce masa.

Ku yi tunanin mutumin dake tsaka da gudanar da baccinsa mai daɗi lokacin tashi bai yi ba, kwatsam sai aka farkar da shi ɓagatatan. Menene zai faru?

• Zai iya tashi lafiya,

• Zai iya firgita ya haɗu da matsala, ko kuma

• Ya tashi da faɗa da ɓacin rai.

Toh haka abin yake ga jinjirin dake cikin mahaifa tsakaninsa da jikin uwar.

Inducement matukar bana lalura bane wanda likitoci da kansu suka hangosa domin aceci rayuwa.... Toh yana buɗe ƙofofin matsaloli da dama: Kama daga matsalar numfashi ga jinjirin da bai gama ƙarasa balaga ba, zuwa matsalar ɓallewar jini da buƙatar yi miki tiyatar (CS) ta gaggawa saboda jiki bai shirya ba. Ba wanda yasan ainihin abin da zai faru dalilin wannan mataki da kuke sha'awar dauka, sai dai kawai abin da aka gani a lokacin.

Haihuwa tsari ne na halitta wanda yake buƙatar haƙuri da lokaci. Kada ku jefa kanku cikin haɗarin da za'a iya kauce masa kurum domin neman sauƙi na ɗan lokaci. Ku bar jiki naturally yai aikinsa a lokacin da ya dace. Rayuwarku data jariranku ta fi ƙarfin abin da za'a yi wa gaggawa.

Wata matsalar ma da akanki kadai zata ƙare shikenan, amma idan inducing yazo da matsala aka shiga Emergency CS galibi classical ne, ba lallai jariri ya rayu ba dama an sallama shi ke ake kokarin ceto, sannan daga nan in classical ne haihuwa da kanki galibi shikenan kuma duk sanda ciki ya samu saide CS, kinga kin jawowa mijinki dawainiyar da ana iya kauce mata.

In abin yazo da tsautsayi mahaifa na iya fashewa ko ta tsage, kinga mafi sauki shine ace acireta inba haka ba ai biyu babu... Kinga ana cire mahaifa ai keda haihuwa saide kiga akuyar gidanku nayi. Toh me yai zafi.

Ciki har zuwa sati 42 is still normal a daka cesa kurum, dole zai fita wataran, kai kwai wanda suke shekara cir da ake cewa Shekarau ƙarin watanni uku ko wajen sati 13 doriya daga normal wata 9 kuma sui hakuri su haihu lafiya. Ku dena gaggawa please, duk numfashi daya da kike lada ne. Da kuna ganin abinda Allah ke baku da bazaku so ku haihun bama.

Allah ya sauki duk wata me ciki lafiya.

Ibrahim Yakubu Yusuf

More from TimesPosts

SABBIN IYAYE KU KOYI HAƘURI | TimesPosts