Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan ’yan Bangladesh biyu bisa aikata lalata a cikin masallaci a Makka
Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan ’yan Bangladesh biyu bisa aikata lalata a cikin masallaci a MakkaMahukuntan Saudiyya sun sanar da kashe wasu ’yan ƙasar Bangladesh biyu bisa zargin aikata…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan ’yan Bangladesh biyu bisa aikata lalata a cikin masallaci a Makka
Mahukuntan Saudiyya sun sanar da kashe wasu ’yan ƙasar Bangladesh biyu bisa zargin aikata lalata a cikin wani masallaci da ke birnin Makka mai alfarma.
Ma’aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inda ta bayyana sunayen waɗanda aka kashe a matsayin Nazrul Islam Abdul Basir da Siti Akhtar, mace.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun kama mutanen biyu bayan faruwar lamarin, inda aka gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu.
A cewar ma’aikatar, kotun da ta saurari shari’ar ta same su da laifi, tare da yanke musu hukuncin kisa bisa tsarin hukunci na Ta’zir, saboda girman laifin da suka aikata da kuma keta alfarmar masallaci.
Ta ƙara da cewa hukumomin shari’a sun tabbatar da hukuncin kafin a samu umarnin sarauta na aiwatar da shi bisa tanade-tanaden Shari’ar Musulunci.
Ma’aikatar ta ce an aiwatar da hukuncin kisan a yankin Makka ranar Laraba.
Ta bayyana cewa matakin ya nuna ƙudirin gwamnatin Saudiyya na tabbatar da tsaro, tabbatar da adalci da kuma aiwatar da dokokin Shari’ar Musulunci kan mutanen da suka keta alfarmar masallatai da mutuncin wasu.
Haka kuma, ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa duk wanda ya aikata irin wannan laifi zai fuskanci hukuncin da Shari’ar Musulunci ta tanada.
More from TimesPosts

Kocin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta 1996 ya ce har yau bai karɓi lambar zinare ta lashe gasar Olympic ba bayan shekaru 30
Kocin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta 1996 ya ce har yau bai karɓi lambar zinare ta lashe gasar Olympic ba bayan shekaru 30Tsohon kocin Super Eagles, Jo Bonfrere, ya ce har yanzu bai karɓi lambar…
Ay Abdullahi1 min read

Da Dumi-Duminsa: Ankai Harin Bama Bamai Kamfanin Sadarwa na Israela Intel a Birnin Kasar na Tel-Aviv
Da Dumi-Duminsa: Ankai Harin Bama Bamai Kamfanin Sadarwa na Israela Intel a Birnin Kasar na Tel-Aviv Fashewa a Kamfanin Intel, Mutane da Dama Sun Ji Rauni Mai TsananiRahotanni daga kafafen yaɗa…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Duniya : Gabashin Duniya
Abun da dakarun Houthis suke yiwa kasar Saudiyya, tun da farko shine abinda Ayatollahi Ali Khomeini yake jiye musu tsoro. Tun yana raye yake ta maimaita musu cewa "Ku musulmai ne 'yan uwan mu, babu…
Ay Abdullahi2 min read