Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Shin Ko Kunsan Suma Haka Ta Faru Dasu Kuwa.....?

China da India duk sun taɓa fama da matsanancin talauci. Amma me ya sauya komai cikin shekaru 40?A shekarun 1980s, China da India suna cikin ƙasashen da ke fama da matsanancin talauci. Amma bayan…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

China da India duk sun taɓa fama da matsanancin talauci. Amma me ya sauya komai cikin shekaru 40?

A shekarun 1980s, China da India suna cikin ƙasashen da ke fama da matsanancin talauci. Amma bayan shekaru 40, China ta fitar da ɗaruruwan miliyoyin mutane yan kasa daga talauci.... India ma ta samu babban ci gaba.

Abin da ya fi ɗaukar hankali kuwa shi ne... Ba hanya daya suka bi ba.

China ta bi nata tsarin.

India ma ta bi nata tsarin daban.

Najeriya da Nijar suna da albarkatu, matasa da damar ci gaba. Amma me ya sa har yanzu talauci yake kara ƙarfi?

Shin matsalar tsarin mulki ce?

Ko ilimi?

Ko ayyukan yi?

Ko masana'antu?

Ko wutar lantarki?

Ko yadda ake tafiyar da tattalin arziki?

Domin albarkatu kaɗai ba sa fitar da ƙasa daga talauci. Abin da ke canza rayuwar mutane shi ne yadda ake amfani da albarkatun wajen samar da ilimi, aiki, masana'antu, da tattalin arzikin da talaka zai iya cin moriyarsa.

Wataƙila ba ma buƙatar sai mun zama China ko India.

Amma ya kamata mu koyi abin da ya yi aiki a wasu wuraren daban-daban, sannan mu gina hanyar da ta dace da mu.

Me kake ganin Najeriya za ta koya daga China da India?

#DigitalPsychologist @topfans

More from TimesPosts

Shin Ko Kunsan Suma Haka Ta Faru Dasu Kuwa.....? | TimesPosts