Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Siyasa Arewachin Nigeria A Yau

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano a gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Hon. Muaz Magaji, ya soki gwamnatin Kano kan abin da ya kira nuna bambanci wajen batun tuhumar tsoffin…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Tsohon Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano a gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Hon. Muaz Magaji, ya soki gwamnatin Kano kan abin da ya kira nuna bambanci wajen batun tuhumar tsoffin gwamnonin jihar kan zargin rashawa.

Muaz Magaji ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce bai kamata gwamnatin jihar ta tsallake tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta mayar da hankali kan tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ba dangane da buƙatar a tuhume shi kan zargin cin hanci da rashawa da cin amana.

Ya ce abin da ke damunsa shi ne dalilin da ya sa aka tsallake Ganduje aka nufi Kwankwaso, yana mai bayyana hakan a matsayin abin da bai dace ba.

Sai dai Muaz Magaji ya jaddada cewa ba yana nufin Kwankwaso bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba ne, amma yana tambayar dalilin da ya sa aka ware shi aka bar wani.

"Ban ce Kwankwaso bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba, amma me ya sa aka tsallake ɗaya aka nufi ɗayan?" In ji Muaz Magaji.

More from TimesPosts