Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran Nigeria A Yau ::: Kotu ta yanke wa ɗan kasuwar man fetur, Jide Omokore da tsoffin ma'aikatan NNPC hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai

Kotu ta yanke wa ɗan kasuwar man fetur, Jide Omokore da tsoffin ma'aikatan NNPC hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke wa hamshaƙin ɗan kasuwar man fetur,…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Kotu ta yanke wa ɗan kasuwar man fetur, Jide Omokore da tsoffin ma'aikatan NNPC hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yanke wa hamshaƙin ɗan kasuwar man fetur, Jide Omokore, da wasu tsoffin shugabannin kamfanin mai na ƙasa (NNPC) hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai kowannensu kan zargin damfarar dala biliyan 1.6.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ta ce kotun ta kuma bayar da umarnin rushe kamfanoni biyu da ke da alaƙa da shari’ar, wato Atlantic Energy Brass Development Limited da Atlantic Energy Drilling Concept Limited.

Sauran waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne Victor Briggs, tsohon manajan daraktan kamfanin NPDC, da Abiye Membere, tsohon babban daraktan NNPC mai kula da harkokin bincike da haƙo mai.

Kotun ta same su da laifi kan tuhume-tuhume tara da suka haɗa da haɗa baki, damfara da halasta kuɗin haram, inda ta ce za su yi zaman gidan yarin a lokaci guda.

EFCC ta zarge su da karkatar da kuɗaɗen da suka samu daga cinikin ɗanyen mai, bayan da Omokore da kamfanoninsa suka ɗauki gangar mai sama da miliyan 7.5 da darajarsu ta kai dala miliyan 823.07, ba tare da biyan kuɗin shiga da sauran haƙƙoƙin da yarjejeniyar ta tanada ba.

A watan Fabrairun 2023 ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta wanke Omokore da kamfanoninsa daga tuhumar, bisa dalilin cewa EFCC ba ta gabatar da isassun hujjoji da za su tabbatar da zargin ba.

Sai dai hukumar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, inda Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta soke hukuncin wankewar tare da yanke wa waɗanda ake tuhuma hukuncin zaman gidan yari.

More from TimesPosts