Siyasa Arewachin Nigeria A Yau :::: Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta buƙaci ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International da ta gudanar da bincike kan kalaman da ake zargin
Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta buƙaci ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International da ta gudanar da bincike kan kalaman da ake zargin tsohon Gwamnan Kano, Sanatasiy Rabiu Musa…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta buƙaci ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International da ta gudanar da bincike kan kalaman da ake zargin tsohon Gwamnan Kano, Sanatasiy Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi, inda ake zargin ya buƙaci magoya bayansa su shirya tunkarar abokan hamayyarsu.
Jam’iyyar ta ce bai kamata binciken ya taƙaita ga mutum ɗaya ko wata jam’iyya ba, inda ta buƙaci Amnesty International ta faɗaɗa bincikenta domin ya shafi dukkan zarge-zargen da suka shafi manyan ’yan siyasa, ba tare da nuna bambanci ba.
Haka kuma, APC ta yi kira ga rundunar ’yan sandan Najeriya da ta gudanar da bincike kan zarge-zargen, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Sai dai, zarge-zargen da ake dangantawa da Kwankwaso na buƙatar cikakken bincike kafin a tabbatar da sahihancinsu.
More from TimesPosts

Siyasa Arewachin Nigeria A Yau. ::: KE DUNIYA INA ZAKI DAMU: Matar da Abba Gida Gida ya kwacewa filaye almost 200 kamar yadda ta fadi da Sauran wasu wa'enda aka kwacewa filaye a Rimin
KE DUNIYA INA ZAKI DAMU: Matar da Abba Gida Gida ya kwacewa filaye almost 200 kamar yadda ta fadi da Sauran wasu wa'enda aka kwacewa filaye a Rimin Zakara dake KH Ungogo Kano ba'a biyasu diyyar…
Ay Abdullahi1 min read

Siyasa Arewachin Nigeria A Yau.
Siyasa fagen gwagwarmaya ce, amma kuma fage ne da ke bukatar amana, hakuri, mutunta juna da kuma tuna wadanda suka taimaka wajen gina mutum har ya kai matsayin da yake alfahari da shi a yau. A…
Ay Abdullahi7 min read

Siyasa Nigeria A Yau ::: A Takaice dai EFCC tazama Karen Farautar Jam'iya mai Mulki.
A Takaice dai EFCC tazama Karen Farautar Jam'iya mai Mulki.... Akwai pettion da muka Rubuta akan Yaron Wike (Minister Abuja) inda muke zarginshi da Damfarar wani client namu, Safwan Garba kusan kudi…
Ay Abdullahi1 min read