Siyasa Duniya : Gabashin Duniya
Abun da dakarun Houthis suke yiwa kasar Saudiyya, tun da farko shine abinda Ayatollahi Ali Khomeini yake jiye musu tsoro. Tun yana raye yake ta maimaita musu cewa "Ku musulmai ne 'yan uwan mu, babu…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

Abun da dakarun Houthis suke yiwa kasar Saudiyya, tun da farko shine abinda Ayatollahi Ali Khomeini yake jiye musu tsoro. Tun yana raye yake ta maimaita musu cewa "Ku musulmai ne 'yan uwan mu, babu fada ko yaki a tsakanin mu. Bama son ku shigo cikin wannan rikicin domin tarko ne America take son dana muku wajen yakar mu. Bama son mu fara kai muku farmaki kan dukiyoyin ku ko wajen ajiye makaman tsaron kasar ku. Ku 'yan uwa ne a gare mu saboda haka kar ku bari ayi amfani da ku wajen ajiye makaman America ko Israela domin kawo mana farmaki. Kar ku bari ayi amfani da sararin samaniyar ku wajen aiko mana da makamai masu linzami. Kar ku bari ayi amfani da al'ummar ku wajen tunzura masu rike da madafun ikon ku domin farmakar 'yan uwan mu musulmai da muke zaune lafiya da ku domin idan hakan ta faru ba zamu zuba muku ido abubuwa su tafi a haka ba. Dole ne zamu dauki matakin kare Kai wanda hakan zai janyo muku asara da tashin hankali idan baku Yi taka tsantsan ba". Wadancan magaganun sune abinda Ayatollahi Ali Khomeini ya yi ta maimaitawa gwamnatin Saudiyya tun da farko amma suka Yi kunnen uwar shegu a zaton su maganar banza ce. Bayan Ayatollahi Ali Khomeini ya yi ta gargadin gwamnatin Saudiyya haka yayi ta maimaitawa sauran kasashen Gulf Countries din nan da suke Middle East amma ba wadda ta saurare shi.
Da gwamnatin Iran ta fahimci abun akwai renin hankali bayan kuma su sun san cewa sun gama shiryawa daman kawai suna gudun kar su fara cin du*run uwar*su ne duniya ta ga cewa basu kyauta ba. A yau mun wayi gari bawai maganar IRGC na Iran ake Yi ba, hatta dakarun Houthis na kasar Yemen wanda sune suke rike da harkokin tsaron Babyl Mandeb su ma sun ce duk wanda ya fasa Allah ya tsine mai Albarka. Daman idan baku manta ba, IRGC sune suke rike da ikon Strait of Hormuz, a yayin da su kuma wadannan dakarun na Houthis kuma sune suke rike da Babyl Mandeb kuma su din ma a karkashin ikon Supreme Leader na Iran din suke. Har zuciya ta bana son wannan rikicin ya dore a Middle East, amma wlh ina baku guarantee matukar gwamnatin Saudiyya da sauran kasashen da suke Middle East basu canza hali ba, na rantse da Allah sai Iran ta kai su gabar da ko ruwa zasu Sha sai an tauna musu. Kananan 'yan iska marasa mutunci. 😒
Salisu Yakubu RN RNT
More from TimesPosts

Da Dumi-Duminsa: Ankai Harin Bama Bamai Kamfanin Sadarwa na Israela Intel a Birnin Kasar na Tel-Aviv
Da Dumi-Duminsa: Ankai Harin Bama Bamai Kamfanin Sadarwa na Israela Intel a Birnin Kasar na Tel-Aviv Fashewa a Kamfanin Intel, Mutane da Dama Sun Ji Rauni Mai TsananiRahotanni daga kafafen yaɗa…
Ay Abdullahi1 min read

Sojoji sun kashe ƴan ISWAP sama da 40 a Borno
Sojoji sun kashe ƴan ISWAP sama da 40 a BornoDakarun rundunar sojin sama ta Operation HADIN KAI sun kashe sama da ƴan ta’addar ISWAP 40 a wani samamen sama da suka kai kauyen Badu da ke ƙaramar…
Ay Abdullahi1 min read

Breaking News : Labaran Duniya Na Gabashin Duniya
LABARI MARAR DADIGwamnatin Kasar Saudiyya ta sanar da rufe filin jirgin saman kasa da kasa na Sarki Khalid bin Abdul-Aziz dake birnin Riyadh sakamakon mummunan hari na ta'addanci da mayakan Houthi…
Ay Abdullahi2 min read