Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 16 a Adamawa

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 16 a AdamawaDakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun ce sun kashe ’yan ta’adda 16 tare da kwato makamai a wasu samame da suka gudanar a Jihar Adamawa.A cewar rahoton…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 16 a Adamawa

Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun ce sun kashe ’yan ta’adda 16 tare da kwato makamai a wasu samame da suka gudanar a Jihar Adamawa.

A cewar rahoton Zagazola Makama, an gudanar da ayyukan tsakanin 30 ga Satumba da 1 ga Oktoba a yankin Sector 4.

Dakarun sun kashe ’yan ta’adda 16 a wani kwanton-bauna da suka yi a yankin Boima, Karamar Hukumar Gombi, inda suka kwato bindigogin AK-47 guda uku, bindigogin pump-action biyu da sauran kayan yaki.

Haka kuma, rundunar sojin sama ta kai hari kan wasu ’yan ta’adda 16 da aka gano tare da babura 15, inda rahoton ya ce harin ya samu inda aka nufa.

Sojojin sun kuma dakile hare-haren ’yan ta’adda kan bataliyar 226 da ke Garkida da ta 232 da ke Garaha.

Sai dai sojoji uku sun mutu yayin artabun, yayin da aka kwashe wadanda suka samu raunuka domin yi musu magani.

Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike da samamen share yankunan da lamarin ya shafa, tare da kira ga jama’a da su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.

More from TimesPosts