Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Wace ƙasa ce Azerbaijan, ƙasar da ke iyaka da Iran kuma mafi rinjayen al'ummarta ƴan Shi'a, amma suke da kyakkyawar alaƙar difilomasiyya da Isra'ila, amma Iran bata taɓa kai mata farmaki ba?

Wace ƙasa ce Azerbaijan, ƙasar da ke iyaka da Iran kuma mafi rinjayen al'ummarta ƴan Shi'a, amma suke da kyakkyawar alaƙar difilomasiyya da Isra'ila, amma Iran bata taɓa kai mata farmaki ba?Ga…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Wace ƙasa ce Azerbaijan, ƙasar da ke iyaka da Iran kuma mafi rinjayen al'ummarta ƴan Shi'a, amma suke da kyakkyawar alaƙar difilomasiyya da Isra'ila, amma Iran bata taɓa kai mata farmaki ba?

Ga dalili..👇

Azerbaijan ƙasa ce da take a yankin Kudancin Caucasus, tsakanin Gabashin Turai da Yammacin Asiya, wadda ake danganta ta da yankin Asiya ta Yamma, ko da yake tana da alaƙa da Turai ta fuskar tarihi da siyasa.

Azerbaijan ta yi iyaka da Rasha ta Arewaci, sannan ta yi iyaka da Georgia da Armenia ta Yammaci.

A yankin Kudancin ƙasar tana iyaka da Iran, yayin da ta yi iyaka da Tekun Caspian ta yankin Gabashi.

Sai dai Azerbaijan ba Larabawa bane ba kuma Turkawa ko Fashawa bane.

Yarensu shi ne Azeri, wanda harshe ne mai zaman kansa kamar kowane Yare, amma ana alaƙanta su da kusanci da Turkawa.

Azerbaijan ta taɓa kasancewa cikin Tarayyar Soviet, kafin ta sake samun ƴancin kanta a shekarar 1991.

Mafi rinjaye na al'ummar Azerbaijan suna gudanar da addini iri ɗaya wato Musulunci, yayin da wasusnsu ke da zafin aƙidar addini, wasu kuma suna ɗaukar Musulunci a matsayin al'adu na iyali.

Haka kuma mafi rinjaye na ƴan ƙasar mabiya addinin Shi’a ne, amma ba masu zafin Shi'anci irin na Iran ba, wanda hakan yasa tsarin mulkinta bai zama na addinin musulunci ba.

Abin tambaya anan shi ne, me yasa Azerbaijan take da kyakkyawar alaƙa da Isra’ila, alhali tana da rinjayen Shi’a?

Dalili shi ne, ƙasashen biyu ba sa yanke dukkan manufofinsu bisa addinin da yawancin al'ummarsu suke bi, sai dai suna sanya manufofin tattalin arziki, tsaro, siyasa da muradun ƙasa ne a gaba fiye da addini.

To me yasa Iran ba ta yaƙar Azerbaijan duk da kasancewarta makusanciya kuma mai kyakkyawar alaƙa da Isra'ila?

Dalili shi ne, Azerbaijan tana gudanar da alaƙar difilomasiyya ne kawai da kasuwanci tsakaninta da Isra'ila.

Misali Azerbaijan tana siyar da man fetur ga Isra’ila, yayin da ita kuma Isra'ilar ke samar da Makamai da Jiragen yaƙi marasa matuƙa, makamai masu linzami da sauran kayan aikin tsaro ga Azerbaijan.

Akwai kuma batun fasahar zamani, Noma da kasuwanci na haɗin gwuiwa a tsakanin ƙasashen.

Azerbaijan bata ba wa Isra'ila damar amfani da wani yanki ko sararin samaniyarta wajen gudanar da ayyukan soji akan Iran ba, wannan yasa Iran bata da niyya ko ƙudurin kai hari cikin Azerbaijan.

Sai dai a ƴan kwanakin nan an soma samun tankiya tsakanin Iran da Azerbaijan ɗin, inda hukumomin Iran suka soma zargin Azerbaijan da neman ƙarfafa alaƙar tsaro da Isra'ila fiye da kima, wanda hakan zai iya kaiwa ga yin amfani da Azerbaijan wajen leƙen asirin cikin gidan Iran.

Sai dai duk da wannan takun saƙa da ya soma ɓullowa, ƙasashen Iran da Azerbaijan suna ci gaba da hulɗa a fannonin cinikayya, sufuri da makamashi.

Saboda haka ba kamar yadda wasu suke zaton cewa, Iran ta ƙi kai farmaki Azerbaijan duk da alaƙarta da Isra'ila saboda ƴan Shi'a ne. A'a, Iran ba zata kai hari Azerbaijan bane saboda Azerbaijan bata ba wa Isra'ila damar yin anfani da ƙasarta wajen gudanar da aikin soji ba.

#AbdulPsychologist

More from TimesPosts