Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato.

Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato.1. Idan aka ce saura kwana ɗaya kacal ka kwananka ya kare...…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato.

1. Idan aka ce saura kwana ɗaya kacal ka kwananka ya kare... wa za ka fara gaya wa? Kuma me za ka ce masa?

2. Idan aka ba ka akwati da ke ɗauke da duk abin da ka taɓa rasawa a rayuwarka, me za ka fara nema a ciki?

3. Wanne ɓangare na kanka ka ka rasa, saboda ƙoƙarin zama mutumin da wasu suke son ka zama?

4. Idan aka ba ka damar zuwa duk inda kake so a duniya yanzu, zaka zabi wanne guri ne?

5. Idan aka ba ka zaɓi biyu ka goge mafi munin abin da ya taɓa faruwa da kai, ko ka maimaita rayuwa a mafi kyawun lokacin da ka taɓa samu, wanne za ka zaɓa?

6. Wane irin tunani ne har yanzu yake yawan dawowa cikin zuciyarka?

7. Idan ka san cewa rayuwarka za ta ƙare bayan shekara ɗaya, wacce damuwar ka ce zata zama bata da muhimmanci yanzu?

8. Idan ɗanka zai rayu daidai irin rayuwar da kake rayuwa yanzu, wane abu za ka ba shi shawarar ya canza?

9. Shin ka taɓa kewar wani lokaci da kayi asarar sa?

Wani lokaci, fahimtar rayuwarka ba ya buƙatar ka canza hanyar da kake bi gaba ɗaya, abin da kake buƙata kawai shi ne ka ɗan tsaya… ka yi shiru… sannan ka yi wa kanka tambayar da ta dace.

#DigitalPsychologist @topfans

More from TimesPosts

Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato. | TimesPosts