Wani mutum mai suna Hitler Mussolini Simeon Flores ya lashe zaɓen magajin gari a ƙasar Peru
Wani mutum mai suna Hitler Mussolini Simeon Flores ya lashe zaɓen magajin gari a ƙasar Peru.Mutumin ɗan takarar wata jam'iyya mai suna Ahora Nación ne, wanda aka zaɓa a garin Queropalca - wani yanki…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Wani mutum mai suna Hitler Mussolini Simeon Flores ya lashe zaɓen magajin gari a ƙasar Peru.
Mutumin ɗan takarar wata jam'iyya mai suna Ahora Nación ne, wanda aka zaɓa a garin Queropalca - wani yanki mai nisa da ke tsakiyar tsaunukan Andes.
Mutanen garin su 229 ne suka zaɓi mutumin mai shekara 45 da haihuwa, kuma ya kayar da ɗan takarar jam'iyyar Renovación Popular Perú da ƙuri'u 25.
Shi dai wannan gari ya kasance mai mutane ƙasa da 1,000, amma abin da ya fi jan hankulan jama'a shine yadda ya ke da sunan mutum biyu da suka yi ƙaurin suna wato marigayi jagoran gwamnatin ƴan Nazi Hitler da abokin tafiyarsa yayin Ƴakin Duniya na Biyu marigayi shugaban Italiya Mussolini.
Alƙaluma daga ofishin zaɓe na ƙasar ta Peru sun tabbatar cewa mutum sama da 700 ne suka ƙada ƙuri'a a zaɓen magajin garin, inda Mista Mussolini ya sami kashi 34 cikin 100 na ƙuri'un.
More from TimesPosts

Kwamishinan ƴansanda na Kano ya bukaci Sarki Aminu Ado ya janye shirin sa na Hawan Fatahu Yakasai
Kwamishinan ƴansanda na Kano ya bukaci Sarki Aminu Ado ya janye shirin sa na Hawan Fatahu Yakasai Kwamishinan ƴansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu…
Ay Abdullahi2 min read
Breaking news KOWA ZAI SH!GA UKU ......
KOWA ZAI SH!GA UKU ..........!ran ta ce nan ba da jimawa ba za ta toshe hanyoyin safarar jiragen ruwa da take ganin ba su da izini a mashigin ruwan Haramuz. Wannan na zuwa ne yayin da Tehran ke ƙara…
Ay Abdullahi1 min read

Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato.
Wani Farfesa daga Japan ya ce... Zan yi maka tambayoyi 9 masu wahala, waɗanda za su taimaka maka ka fahimci kanka fiye da yadda kake zato.1. Idan aka ce saura kwana ɗaya kacal ka kwananka ya kare...…
Ay Abdullahi1 min read