Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Babbar kotun jihar Kano da ke Bompai karkashin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da daurin aiki mai wahala, bayan samunsu da laifin kisan

Babbar kotun jihar Kano da ke Bompai karkashin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da daurin aiki mai wahala, bayan samunsu da laifin kisan…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

Babbar kotun jihar Kano da ke Bompai karkashin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da daurin aiki mai wahala, bayan samunsu da laifin kisan wata matar aure da ƴaƴanta shida.

Wadanda kotun ta tabbatar da laifinsu sun hada da Umar Auwalu da Yakubu Dayyabu, wadanda aka kama da laifuka bakwai da suka hada da kisan gillar da suka yi wa marigayiya Fatima Abubakar da kananan yaranta a gidansu da ke Dorayi Chiranchi a watan Janairun bana.

A yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya bayyana cewa masu shigar da kara sun gabatar da kwararan hujjoji da suka tabbatar da cewa matasan biyu ne suka aikata wannan mummunan laifi ba tare da wata shakka ba.

A gefe guda kuma, kotun ta wanke tare da sallamar mutum na uku da ake zargi, Isyaku Dayyabu wanda aka fi sani da Chebe, sakamakon gaza samun hujjojin da suka hada shi da wannan danyen aiki.

Wannan hukunci ya kawo karshen shari’ar da ta jima tana tayar da hankulan al’ummar Kano tun bayan faruwar lamarin a ranar 17 ga watan Janairu, inda mutane da dama suka nuna gamsuwarsu da yadda shari'ar ta gudana.

More from TimesPosts

Babbar kotun jihar Kano da ke Bompai karkashin Mai Shari’a Nasiru Saminu, ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da daurin aiki mai wahala, bayan samunsu da laifin kisan | TimesPosts