Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Duniya Jarumta. ::: DAGA Jarumin Ƙwallon Ƙafa Zuwa Ga Mutumin Da Ya Yi Gwagwarmaya Domin Ceto Iyalansa… Labari Ne Mai Tausayar Zuciya. 🥺❤️

DAGA Jarumin Ƙwallon Ƙafa Zuwa Ga Mutumin Da Ya Yi Gwagwarmaya Domin Ceto Iyalansa… Labari Ne Mai Tausayar Zuciya. 🥺❤️Tsohon Fitaccen Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙafar Najeriya, Tijani Babangida, Ya Sake…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

DAGA Jarumin Ƙwallon Ƙafa Zuwa Ga Mutumin Da Ya Yi Gwagwarmaya Domin Ceto Iyalansa… Labari Ne Mai Tausayar Zuciya. 🥺❤️

Tsohon Fitaccen Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙafar Najeriya, Tijani Babangida, Ya Sake Samun Dalilin Farin Ciki Bayan Shafe Sama Da Shekaru Biyu Yana Cikin Mawuyacin Hali.

A Watan Mayun 2024, Wani Mummunan Haɗarin Mota Ya Yi Sanadin Rasuwar Ɗansa Ƙarami, Fadil, Da Ƙaninsa, Ibrahim. Shi Kuma Tijani Ya Samu Munanan Raunuka, Yayin Da Matarsa, Maryam, Ta Samu Munanan Raunuka A Fuska, Ta Rasa Ido Guda, Sannan Ta Rasa Ƙwaƙwalwar Abin Da Ya Faru A Lokacin Haɗarin.

Bayan Watanni Uku, Lokacin Da Tijani Ya Sanar Da Maryam Cewa Sun Rasa Ɗansu, Rahotanni Sun Bayyana Cewa Maryam Ta Tambaye Shi: “Menene Sunansa?”

Sai Dai Duniyar Ƙwallon Ƙafa Ba Ta Yi Watsi Da Ɗaya Daga Cikin Nata Ba. Tsofaffin Abokan Wasansa A Ajax, Roda JC Da VVV-Venlo, Tare Da Abokansa Da Sauran Al’ummar Ƙwallon Ƙafa, Sun Haɗa Kai Domin Taimaka Wa Iyalin.

An Ƙiyasta Kuɗin Jinyar Maryam Da Aikin Gyaran Fuskarta A Ƙasar Netherlands Da Yuro 170,000.

Yanzu, Bayan Sama Da Shekaru Biyu Na Jinya, Tiyata Da Gwagwarmayar Rayuwa, Ga Su Nan Cikin Murmushi. Maryam Tana Murmushi, Tijani Yana Dariya, Yayin Da Ƙaramar ’Yarsu Ta Ƙara Musu Wani Sabon Dalilin Farin Ciki.

Duk Da Cewa Ba Za Su Sake Dawo Da Waɗanda Suka Rasa Ba, Amma Sun Sake Samun Wani Abu Mai Girma A Tsakiyar Wannan Bala’i: SOYAYYA, ABOTA Da TAIMAKON JUNA.

Ƙwallon Ƙafa Ba Wai Kofuna, Ƙwallaye Da Hamayya Kawai Ba Ne. A Wasu Lokuta, Manyan Nasarorinta Suna Faruwa Ne A Wajen Filin Wasa.

MUNA GIRMAMA DUK WANDA YA TSAYA TARE DA IYALAN BABANGIDA A WANNAN MUMMUNAN LOKACI. ❤️🙏

ALLAH YA JIKAN FADIL DA IBRAHIM. YA SANYA SU CIKIN ALJANNAH. 🕊️

More from TimesPosts

Duniya Jarumta. ::: DAGA Jarumin Ƙwallon Ƙafa Zuwa Ga Mutumin Da Ya Yi Gwagwarmaya Domin Ceto Iyalansa… Labari Ne Mai Tausayar Zuciya. 🥺❤️ | TimesPosts