Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Sarkin Kano ya buƙaci ƴan Najeriya su faɗaɗa hanyoyin zuba jari bisa tsarin addinin musulunci

Sarkin Kano ya buƙaci ƴan Najeriya su faɗaɗa hanyoyin zuba jari bisa tsarin addinin musulunci Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci ƴan Najeriya da masu kasuwanci su faɗaɗa hanyoyin adana…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Sarkin Kano ya buƙaci ƴan Najeriya su faɗaɗa hanyoyin zuba jari bisa tsarin addinin musulunci

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci ƴan Najeriya da masu kasuwanci su faɗaɗa hanyoyin adana kuɗaɗensu da zuba jari ta hanyar amfani da tsare-tsaren kuɗi da suka dace da ƙa’idojin Musulunci.

Sanusi ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da asusun zuba jari na UTLAM Halal Fund, tare da buɗe ofisoshin kamfanonin UTL Trust Management Services Limited da UTL Asset Management Limited a Kano ranar Litinin.

Asusun na ba masu zuba jari damar amfani da ƙwararrun hanyoyin sarrafa kuɗi domin samar da arziki ta hanyar zuba jari da ya dace da Shari’ar Musulunci.

Sarkin ya ce ya kamata mutane su wuce tsarin ajiye kuɗi kawai a bankuna ko amfani da asusun lamuni, su rungumi wasu hanyoyin kuɗi da suka haɗa da inshora da zuba jari domin kare dukiyoyinsu da gina kyakkyawar makoma ga iyalansu.

Ya ce wasu ’yan kasuwa a Kano sun yi asarar dukiyoyi masu yawa sakamakon gobara, sata da zagon ƙasa, inda wasu suka tilasta rufe sana’o’insu saboda rashin samun isassun hanyoyin kuɗi da za su taimaka musu wajen farfaɗowa bayan asara.

Sanusi ya ƙara da cewa akwai hanyoyin zuba jari da suka dace da ƙa’idojin Musulunci waɗanda za su taimaka wa ’yan kasuwa wajen kare dukiyoyinsu da inganta tsaron kuɗaɗensu.

A nasa jawabin, shugaban kamfanin UTL, Dakta Shamsuddeen Usman, ya ce buɗe ofishin Kano ba wai kawai ƙara yawan rassan kamfanin ba ne, illa ƙoƙarin kusantar da ayyukansu ga mazauna jihar.

Usman ya bayyana cewa kamfanin ya ƙaddamar da ayyukan kuɗi da suka dace da Shari’ar Musulunci ga abokan hulɗarsa a Kano, bayan kwamitin ba da shawara kan Shari’a na kamfanin ya tantance tare da amince da su.

Ya ce ofishin Kano zai samar da ayyuka da suka haɗa da kula da amana da dukiya, rubuta wasiyya da sauran hanyoyin zuba jari da suka dace da Shari’ar Musulunci ga daidaikun mutane da hukumomi.

More from TimesPosts