Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Nishadi Zallah. ::: YAUSHE ZA KI YI AURE?” KIN ƘI AURE? KADA KI AJIYE WAƊANNAN KALAMAN A ZUCIYARKI, KANWATA!

“YAUSHE ZA KI YI AURE?” KIN ƘI AURE? KADA KI AJIYE WAƊANNAN KALAMAN A ZUCIYARKI, KANWATA!’Yar uwa, wataƙila kin saba jin ana tambayarki: “Yaushe za ki yi aure?” Wasu suna tambaya ne cikin wasa, wasu…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

“YAUSHE ZA KI YI AURE?” KIN ƘI AURE? KADA KI AJIYE WAƊANNAN KALAMAN A ZUCIYARKI, KANWATA!

’Yar uwa, wataƙila kin saba jin ana tambayarki: “Yaushe za ki yi aure?” Wasu suna tambaya ne cikin wasa, wasu kuma suna faɗin kalaman da suke sa ki ji kamar kin gaza a rayuwa saboda har yanzu ba ki yi aure ba.

Wani ya ce: “Ai shekarunki suna tafiya.” Wata ta ce: “Duk ƙawayenki sun yi aure, ke har yanzu kina nan.” Wani kuma ya ce: “Wataƙila ba kya samun miji ne saboda wani abu.”

Kanwata, ina so ki fahimci abu ɗaya: Kada ki bari maganganun mutane su zama nauyin da za ki ɗauka a zuciyarki.

Aure ba gasar da ake yi da ƙawayenki ba ce. Ba wai duk wadda ta yi aure da wuri ta fi samun nasara ba ce, haka kuma rashin yin aure a yanzu ba yana nufin kin rasa darajarki ba ne.

Kada ki yi aure saboda kawai kin gaji da tambayoyin mutane. Kada ki karɓi mutumin da ba ki gamsu da halinsa ba saboda tsoron a ce kin ƙi aure.

Ki tuna, waɗanda suke tambayarki yau ba su ne za su zauna da ke a cikin gidan auren ba. Ke ce za ki rayu da zaɓin da kika yi.

Ki ci gaba da gyara kanki, ki nemi ilimi, ki inganta rayuwarki, ki yi addu’a, ki kuma buɗe ƙofa ga aure idan kin samu mutumin kirki mai tsoron Allah, mutunci, amana da alhakin iyali.

Idan wani ya tambaye ki yaushe za ki yi aure, ki amsa cikin natsuwa. Ba sai kin yi faɗa ba, kuma ba sai kin ji kunyar halin da kike ciki ba.

Kanwata, kada ki auri mutum domin ki rufe bakin mutane. Ki yi aure ne domin kin samu wanda za ku iya gina rayuwa tare cikin mutunci da tausayi.

Allah Ya ba duk mai neman aure miji nagari, Ya kuma ba waɗanda suke jira haƙuri da kwanciyar hankali.

✍️ Dr Ibrahim Hudu Marubuci

Idan wannan ya taɓa zuciyarki, ki turawa wata ’yar uwa domin ita ma ta amfana.

More from TimesPosts