Labaran Duniya Daga timesposts :: Gabas ta Tsakiya. KASAR |RAN TA KURE DABARUN AMURKA
KASAR |RAN TA KURE DABARUN AMURKAWani abu mai kama da abin kunya, zubar da kima, da nuna gazawa da kure dabarun yaki na Amurka ya faru awanni 7 da suka gabataBabbar rundunar sojin Amurka wanda take…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

KASAR |RAN TA KURE DABARUN AMURKA
Wani abu mai kama da abin kunya, zubar da kima, da nuna gazawa da kure dabarun yaki na Amurka ya faru awanni 7 da suka gabata
Babbar rundunar sojin Amurka wanda take kula da harkokin tsaro, ayyukan Soji da dabarun kare muradun Amurka a yankin Kasashen Larabawa da wasu sassan Asiya, wanda ake kira US Central Command (CENTCOM), ta fitar da sanarwa awanni 7 da suka gabata
Sanarwan na cewa Gwamnatin Amurka zata bayar da tukwicin kudi Dalar Amurka Miliyan 20, kimanin Naira Biliyon 28 ga duk wanda bayar da sahihan bayanan sirri akan inda Kasar Iran take kera Makamin Nukiliya
Bayanan da ake nema sun hada da: (1) Guraren da Iran take gudanar da ayyukan Nukiliyarta
(2) kayayyakin aikin Nukiliyar Iran
(3) Na'urorin da ake amfani da su don kera Makamin Nukilya
(4) Mutanen da ke da alaka da shirin Nukiliyar Iran
(5) Masana ilimin kimiyyar Nukiliya na Ira
(6) Bayanan motsi da jigilar duk wani abu dake da alaka da shirin Nukiliya na Kasar Iran
Sannan kuma sunce duk wanda ya bada bayanan sirrin Nukiliyar Iran, idan a cikin Iran yake da zama, za'a canza masa gurin zama, kuma za'a bashi cikakken kariya bayan an bashi tukwicin kudi Dalar Amurka Miliyan 20
Wannan sanarwa na rundinar Sojin Amurka yana bayyana mana cewa Iran ta gama kure wayo da dabarun tsaron Amurka musamman a bangaren Spy da Intelligence, gaskiya na jinjina wa Kasar Iran Wallahi
Wai me zai hana Iran ba zasuyi watsi da tafarkin Shi'ah su dawo Sunnah bane?, da zasuyi haka da sun hadu da taimakon Allah fiye da wanda suke samu a yanzu
Yaa Allah Ka tabbatar wa |ran cikakken na$ara a kan taron dangin ¥ah0dawan duniya
More from TimesPosts

Labaran siyasa :: BINCIKE: Yadda gwamnan Kano, Abba, ya nemi a sauya Kwamishinan ƴansanda da DPO 18 gabanin zaɓen 2027
BINCIKE: Yadda gwamnan Kano, Abba, ya nemi a sauya Kwamishinan ƴansanda da DPO 18 gabanin zaɓen 2027Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nemi a sauya wurin aiki na Kwamishinan ’yansandan jihar,…
Ay Abdullahi2 min read

Labaran Duniya. Zanga-zangar ƴan bana-bakwai ta rikide zuwa rikici a manyan biranen Jamus
Zanga-zangar ƴan bana-bakwai ta rikide zuwa rikici a manyan biranen JamusZanga-zangar matasan Jamus ƴan bana-bakwai wato Gen Z ta rikide zuwa tarzoma da satar kayayyaki a wasu manyan biranen ƙasar,…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya ::: SUN ZALUNCI SPAIN.
SUN ZALUNCI SPAIN.Akwai manyan dalilai guda biyu da suka sa wasu masu sharhi a kafafen sada zumunta ke zargin I$ra'!la da hannu a shirya mummunan haɗurran jiragen ƙasa da suka faru a Spain, duk da…
Ay Abdullahi2 min read