Labaran Duniya :: Kasar Saudiyya. Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure ba
Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure baWata kotun ƙasar Saudiyya ta yanke wa wata ƴar aikin gida 'yar Kenya mai shekaru 40, Esther Wanja…
Ay Abdullahi · Admin
· 2 min read

Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure ba
Wata kotun ƙasar Saudiyya ta yanke wa wata ƴar aikin gida 'yar Kenya mai shekaru 40, Esther Wanja Muthoni, hukuncin bulala 100 bisa laifin yin jima'i ba tare da aure ba, bayan ta haifi ɗa a ƙasar.
An yanke hukuncin ne a watan Oktoban 2026, bayan zaman shari'a da dama, lamarin da ya jefa matar cikin fargaba yayin da take ƙoƙarin komawa ƙasarta tare da ɗanta mai shekara guda.
Jaridar The New York Times ta rawaito cewa Muthoni ta samu juna biyu ne bayan wata gajeriyar alaƙa da wani ɗan ƙasar Masar da ke zaune a Saudiyya, wanda aka bayyana da suna Mohamud.
Ta haifi ɗanta mai suna Abudy a watan Agustan 2025 a gidan kwanan ma'aikata, inda daga bisani aka kai ta asibiti tare da jaririn, sannan 'yansanda suka tsare ta domin yi mata tambayoyi.
Rahotanni sun ce bayan sakin ta, an hana ta komawa masaukin aikinta ko samun matsuguni a wani gidan kula da mata, lamarin da ya tilasta mata zama a wani gidan mai da ke Riyadh.
Daga baya, kamfanin da ta yi wa aiki ya samar mata da masauki, yayin da ofishin jakadancin Kenya ya ba ta takardun da za su taimaka mata wajen komawa gida. Sai dai shari'ar da ake yi mata ta hana ta barin Saudiyya.
Rahoton ya bayyana cewa Muthoni ba ta da lauya yayin shari'ar, duk da cewa an samar mata da mai fassara.
Wata masaniyar ƙaura da ƙwadago, Ekaterina Porras Sivolobova, ta soki hukuncin, tana mai cewa bulala ya saɓa wa ƙa'idojin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa.
Baya ga hukuncin bulala 100, kotun ta kuma yanke mata hukuncin shekara guda na korar ta daga yankin da take zaune, sai dai ba a fayyace ko hakan na nufin mayar da ita Kenya ba.
Muthoni ta ce ba ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin ba, domin babban burinta shi ne komawa gida domin haɗuwa da sauran 'ya'yanta.
More from TimesPosts

Labaran Duniya. ::: Mai yake Faruwa A Arewachin Nigeria. AN KASHE SHUGABAN MIYETTI ALLAH
AN KASHE SHUGABAN MIYETTI ALLAHAn yi babban rashi sakamakon mutuwar Alhaji Ibrahim Dio, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Cattle Association ta Karamar Hukumar Takum jihar TarabaMarigayin ya dawo gida…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya. : ko Kunsan A yanzu A Nigeria Akwai Layikan sadarwa na waya a Najeriya sun haura miliyan 200 a karon farko
Layikan sadarwa na waya a Najeriya sun haura miliyan 200 a karon farkoAdadin layukan sadarwar waya da ke aiki a Najeriya ya kai miliyan 200.3 a watan Satumban 2026, a karon farko tun bayan matakin…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya Na Gabashin Duniya :: Mai ke shirin faruwa
Lahaula walaƙuwwata......✊Malam babban goro dole sai magogin ƙarfe wlh. Idan baku manta ba, a kwanakin baya ƙasar Iran ta taɓa harba wata ƙirƙirarriyar fasahar sadarwa sama da guda 200 sararin…
Ay Abdullahi2 min read