Labaran Duniya. : ko Kunsan A yanzu A Nigeria Akwai Layikan sadarwa na waya a Najeriya sun haura miliyan 200 a karon farko
Layikan sadarwa na waya a Najeriya sun haura miliyan 200 a karon farkoAdadin layukan sadarwar waya da ke aiki a Najeriya ya kai miliyan 200.3 a watan Satumban 2026, a karon farko tun bayan matakin…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Layikan sadarwa na waya a Najeriya sun haura miliyan 200 a karon farko
Adadin layukan sadarwar waya da ke aiki a Najeriya ya kai miliyan 200.3 a watan Satumban 2026, a karon farko tun bayan matakin tilasta haɗa lambar NIN da katin SIM da ya janyo katsewar layuka da dama a shekarar 2024.
Bayanan Hukumar Kula da Sadarwa ta Ƙasa (NCC) sun nuna cewa layukan sun ƙaru daga miliyan 197.4 a watan Agusta zuwa 200,337,097 a watan Satumba, wanda ke nuna ƙarin layuka kusan miliyan 2.9.
Bayanan sun kuma nuna cewa yawan yaɗuwar sadarwar waya a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 92.41 cikin 100, daga kashi 91.07 a watan Agusta.
Dangane da fasahar sadarwa, 4G ce ta fi rinjaye da kashi 54.37, sai 2G mai kashi 36.42, yayin da 3G ke da kashi 4.16. Fasahar 5G kuma ta ƙaru zuwa kashi 5.05 daga kashi 4.92.
Haka kuma, adadin masu amfani da intanet ya ƙaru zuwa miliyan 160.9 daga miliyan 158.5, yayin da masu amfani da babbar hanyar intanet (Broadband) suka kai miliyan 128.
Sai dai yawan bayanan intanet da aka yi amfani da su ya ragu zuwa terabytes miliyan 1.73 a watan Satumba, daga miliyan 1.76 a watan Agusta.
Rahoton ya kuma nuna cewa gudummawar ɓangaren sadarwa ga tattalin arzikin Najeriya (GDP) ta ƙaru zuwa kashi 9.72 a zangon farko na biyu na shekarar 2026, daga kashi 9.19 a zangon farko na shekarar.
Haka kuma, MTN ce ta fi samun sababbin kwastomomi da suka sauya layukansu zuwa kamfanin, inda ta samu 854, sai Airtel mai 580, Globacom mai 165, yayin da Vitel ya samu huɗu.
More from TimesPosts

Labaran Duniya :: Kasar Saudiyya. Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure ba
Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure baWata kotun ƙasar Saudiyya ta yanke wa wata ƴar aikin gida 'yar Kenya mai shekaru 40, Esther Wanja…
Ay Abdullahi2 min read

Labaran Duniya. ::: Mai yake Faruwa A Arewachin Nigeria. AN KASHE SHUGABAN MIYETTI ALLAH
AN KASHE SHUGABAN MIYETTI ALLAHAn yi babban rashi sakamakon mutuwar Alhaji Ibrahim Dio, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Cattle Association ta Karamar Hukumar Takum jihar TarabaMarigayin ya dawo gida…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya Na Gabashin Duniya :: Mai ke shirin faruwa
Lahaula walaƙuwwata......✊Malam babban goro dole sai magogin ƙarfe wlh. Idan baku manta ba, a kwanakin baya ƙasar Iran ta taɓa harba wata ƙirƙirarriyar fasahar sadarwa sama da guda 200 sararin…
Ay Abdullahi2 min read