Labaran Duniya. ::: Mai yake Faruwa A Arewachin Nigeria. AN KASHE SHUGABAN MIYETTI ALLAH
AN KASHE SHUGABAN MIYETTI ALLAHAn yi babban rashi sakamakon mutuwar Alhaji Ibrahim Dio, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Cattle Association ta Karamar Hukumar Takum jihar TarabaMarigayin ya dawo gida…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

AN KASHE SHUGABAN MIYETTI ALLAH
An yi babban rashi sakamakon mutuwar Alhaji Ibrahim Dio, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah Cattle Association ta Karamar Hukumar Takum jihar Taraba
Marigayin ya dawo gida lafiya daga Kasuwar Shanu ta Takum da yamma, va da jimawa ba, wasu mahara da suka zo a kan babur suka isa gidansa da ke Unguwar Abuja, Layin Makarantar Rogo Primary School Takum suka harbe shi har lahira
Alhaji Ibrahim Dio ya kasance shugaba mai kishin al’ummarsa, musamman Fulani da sauran mazauna Takum, kuma mutum ne da aka bayyana wanda yake da kyakkyawar mu’amala da mutane, sannan yana jagorantar sulhu da dakile rikicin fulani da manoma
Watakila wannan ne ba sa so sai makiya zaman lafiya suka biyoshi har gida suka harbe shi da bindiga
Muna rokon Allah Ya jikansa, Ya tona asirin wadanda suke da hannu a kisan sa
More from TimesPosts

Labaran Duniya :: Kasar Saudiyya. Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure ba
Kotu a Saudiyya ta yankewa wata 'yar Kenya hukuncin bulala 100 kan yin jima'i ba tare da aure baWata kotun ƙasar Saudiyya ta yanke wa wata ƴar aikin gida 'yar Kenya mai shekaru 40, Esther Wanja…
Ay Abdullahi2 min read

Labaran Duniya. : ko Kunsan A yanzu A Nigeria Akwai Layikan sadarwa na waya a Najeriya sun haura miliyan 200 a karon farko
Layikan sadarwa na waya a Najeriya sun haura miliyan 200 a karon farkoAdadin layukan sadarwar waya da ke aiki a Najeriya ya kai miliyan 200.3 a watan Satumban 2026, a karon farko tun bayan matakin…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya Na Gabashin Duniya :: Mai ke shirin faruwa
Lahaula walaƙuwwata......✊Malam babban goro dole sai magogin ƙarfe wlh. Idan baku manta ba, a kwanakin baya ƙasar Iran ta taɓa harba wata ƙirƙirarriyar fasahar sadarwa sama da guda 200 sararin…
Ay Abdullahi2 min read