Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran siyasa. ::: INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027

INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027Hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta kasa (INEC) za ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen wasu ‘yan takarar gwamna da aka cire sunayensu…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027

Hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta kasa (INEC) za ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen wasu ‘yan takarar gwamna da aka cire sunayensu daga jerin waɗanda za su fafata a zaɓen 2027.

Daga cikin ‘yan takarar akwai tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, na jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, da Abdulsalam Gwarzo na jam’iyyar NDC a Kano, da Sanata Danjuma Laah na Kaduna, da Sebastine Hon na SDP a Benue.

Wata majiya a INEC ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa hukumar za ta tattauna batun a taronta na yau, Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026.

INEC ta bayyana cewa ta cire wasu ‘yan takara ne saboda jam’iyyunsu sun gaza gabatar da rajistar mambobinsu kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2026 ta tanada.

Matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, wanda ya tabbatar da wajabcin gabatar da rajistar mambobin jam’iyyu kafin gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani.

Hukumar ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafen waɗanda abin ya shafa kafin wa’adin da aka kayyade na 24 ga Oktoba, kuma sassan da abin ya shafa suna nazarinsu domin ɗaukar matakin da ya dace bisa doka.

More from TimesPosts

Labaran siyasa. ::: INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027 | TimesPosts