Labaran Siyasa :: Na taɓa zama direban tasi dan kawai na biya wa kaina kuɗin makaranta - Tinubu
Na taɓa zama direban tasi dan kawai na biya wa kaina kuɗin makaranta - Tinubu Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya taɓa yin aikin tuƙin taxi da wasu ayyuka daban-daban a ƙasar Amurka…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Na taɓa zama direban tasi dan kawai na biya wa kaina kuɗin makaranta - Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya taɓa yin aikin tuƙin taxi da wasu ayyuka daban-daban a ƙasar Amurka domin samun kuɗin biyan karatunsa na jami’a.
Tinubu ya ce bayan saukar sa a Amurka, ya jinkirta fara karatu na wasu watanni domin tara kuɗin makaranta.
Ya bayyana cewa irin waɗannan ƙalubale ne suka sa gwamnatinsa ke ƙoƙarin inganta damar samun ilimi ga kowane ɗan Najeriya.
Shugaban ya bayyana cewa Asusun Tallafa wa Ɗalibai na NELFUND ya bayar da rancen kuɗi sama da Naira biliyan 372 domin taimaka wa ɗalibai wajen biyan kuɗin makaranta da sauran buƙatunsu.
Ya kuma bayyana cewa:
Sama da mutane miliyan 2.8 sun nemi shiga shirin koyon sana’o’i da fasaha.
An gyara kwalejojin fasaha guda 38.
Ana kashe Naira biliyan 110 wajen gyaran makarantun koyon aikin likitanci guda 24.
Adadin ɗaliban aikin jinya ya ƙaru daga 28,000 zuwa 115,000.
Sama da yara miliyan ɗaya da ba sa zuwa makaranta sun koma karatu.
Tinubu ya kuma ce gwamnatinsa ta cimma sabon yarjejeniya da ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU), wadda ta ƙunshi ƙarin kashi 40 cikin 100 na albashin malaman jami’a.
Ya jaddada cewa burinsa shi ne ganin ɗalibai sun kammala karatunsu a kan lokaci, tare da samar da ingantaccen ilimi ga kowane yaro ba tare da la’akari da halin kuɗin iyayensa ba.
More from TimesPosts

Obama ya bukaci yan jam'iyyar Democrat su yi amfani da nasarar zabukan su wajen kawo sauyi a Amurka
Obama ya bukaci yan jam'iyyar Democrat su yi amfani da nasarar zabukan su wajen kawo sauyi a Amurka Tsohon shugaban kasar Amurka Barack obama ya bukaci yan jam’iyyar Democrat da suyi amfani da ikon…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran siyasa. ::: INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027
INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027Hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta kasa (INEC) za ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen wasu ‘yan takarar gwamna da aka cire sunayensu…
Ay Abdullahi1 min read

Ɗan majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi iƙirarin cewa albashin sabon ma’aikacin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya ninka nasa sau 3
Ɗan majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi iƙirarin cewa albashin sabon ma’aikacin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya ninka nasa sau 3.Doguwa, wanda ke…
Ay Abdullahi1 min read