Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Labaran Wasani

🗞️ LABARI 💥 Cesc Fàbregas ya ce ya yi nadamar umartar ƴan wasan sa su rage zafin fafatawa lokacin da Como ke kan gaba da Manchester United da ci 4-0. Ya ce ya yi hakan ne domin su adana ƙarfin su…

Ay Abdullahi · Admin

· 1 min read

🗞️ LABARI 💥 Cesc Fàbregas ya ce ya yi nadamar umartar ƴan wasan sa su rage zafin fafatawa lokacin da Como ke kan gaba da Manchester United da ci 4-0. Ya ce ya yi hakan ne domin su adana ƙarfin su don wasan da ke tafe.

Fàbregas ya ce:

“Na yi nadamar abin da ya faru a mintuna 10 na ƙarshe, domin ni ne na umarci ƙungiyar ta rage saurin wasa, saboda muna da wani wasa a gaba. Da muka ci 4-0, na ga za mu iya ɗan sassauta yadda muke tafiyar da wasan.

“Na gaya wa ƴan wasan su daina yawan gudu, su tsaya a tsakiyar fili. Wannan abu ne da na yi nadama a kai, domin ni ne mutum na farko da kullum yake ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da fafatawa da dukkan ƙarfin su har a tashi daga wasa.

“Ƙwallon da Manchester United ta ci ta ɓata min rai, domin mun rage zafin yadda muke buga wasan, sannan muka sassauta tsaron baya. Amma laifin nawa ne.”

Tushe:Reddit,Footballitarin

More from TimesPosts

Labaran Wasani | TimesPosts