Labaran Wasani :: Yunƙurin da Kylian Mbappé da Lamine Yamal suka kwashe watanni biyu suna yi na jan hankalin kafafen yaɗa labarai
LABARI 💥 Yunƙurin da Kylian Mbappé da Lamine Yamal suka kwashe watanni biyu suna yi na jan hankalin kafafen yaɗa labarai domin ƙara wa kansu damar lashe kyautar Ballon d’Or, mai yiwuwa ya zama…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

LABARI 💥 Yunƙurin da Kylian Mbappé da Lamine Yamal suka kwashe watanni biyu suna yi na jan hankalin kafafen yaɗa labarai domin ƙara wa kansu damar lashe kyautar Ballon d’Or, mai yiwuwa ya zama sanadin da ya yi musu illa maimakon ya taimaka musu.
A gefe guda kuma, Harry Kane ya nuna dattako da mutunta kan shi a duk tsawon lokacin. Ya bar bajintar sa a filin wasa da ƙididdigar ƙwallayen da ya ci su yi masa alƙalanci, ba tare da ya yi wani yunƙuri na rage darajar sauran ƴan takarar ba.
Wannan salo nasa ya burge ƴan jaridun da ke kaɗa ƙuri’a wajen zaɓen wanda zai lashe babbar kyautar ɗan wasa ɗaya tilo a ƙwallon ƙafa, kuma mai yiwuwa hakan ne ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Harry Kane.
Tushe: ESPN,Gazetta dello sport, The independent
More from TimesPosts

Labaran Wasani :: BARCELONA KA IYA FISKANTAR HUKUNCI BAYAN JIFAN YAN WASAN REAL MADRID A DAREN JIYA.
LABARI💥BARCELONA KA IYA FISKANTAR HUKUNCI BAYAN JIFAN YAN WASAN REAL MADRID A DAREN JIYA. Ƙungiyar FC Barcelona na iya fuskantar hukunci daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Spain bayan da wasu daga cikin…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Wasani :: LABARI💥KYLIAN MBAPPE ZAI IYA ZAMA DAN WASA NA 7 DA YA LASHE KYAUTAR BALAND'O BA TARE DA LASHE KOFI BA.
LABARI💥KYLIAN MBAPPE ZAI IYA ZAMA DAN WASA NA 7 DA YA LASHE KYAUTAR BALAND'O BA TARE DA LASHE KOFI BA. Wasu mutane na ganin cewa kamar idan dan wasa Kylian Mbappe ya lashe kyautar baland'or kamar…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Wasani. ::: Mai tsaron ragar Arsenal, David Raya, ya bayyana cewa yana matuƙar sha’awar buga wasa a gasar La Liga ta Sifaniya a nan gaba.
LABARI 💥 Mai tsaron ragar Arsenal, David Raya, ya bayyana cewa yana matuƙar sha’awar buga wasa a gasar La Liga ta Sifaniya a nan gaba. David Raya ya ce:“Eh, ina matuƙar son hakan. Ina son in gwada…
Ay Abdullahi1 min read