Nasiha ::: shin ko kunasa Wanna batu kuwa ...
JAN HANKALI: Ana yawan yaudarar matasa da sunan aiki a ƙasashen waje kamar Lìbya, Algeria, da wasu ƙasashe masu wahalar rayuwa. Ana kiran mutane da cewa "za a kai ka company" ko "akwai aiki wanda ake…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

JAN HANKALI: Ana yawan yaudarar matasa da sunan aiki a ƙasashen waje kamar Lìbya, Algeria, da wasu ƙasashe masu wahalar rayuwa. Ana kiran mutane da cewa "za a kai ka company" ko "akwai aiki wanda ake sumun kudi sosai. yawanci ƙarya ce! Yaudara ce! Tarko ne!
Ka sani cewa, kasarka ita ce gidanka kuma duk abinda kake nema a kasarka zaka iya samu idan Allah ya yarda, sai dai idan, rabonka daman a chan yake, inda za ka tafi, ba ka da yanci.
Inda kana da wata sana'a da kake yi anan gida gwara kayi hakuri ka rike da kyau, idan kayi hakuri ka dage wata rana zakayi nasara.
Chan idan zaka tafi, ba ka da dangi. Ba ka da wanda zai tsaya maka.
Muna kira ga duk wanda ke shirin tafiya ta hannun waɗannan agents:
Ka Tsaya Kayi Tunani Kayi Bincike akai
Kar ka bari a dauke ka daga ƙasarka har zuwa wurin da ba ka san komai ba. Kar ka bari a yaudare ka da alkawuran da ba su da tushe. Kar ka bar iyayenka da 'yan uwanka cikin dimuwa ba tare da sun san wani hali kake ciki ba.
Idan ka san wani Dan uwanka yana shirin tafiya irin wannan ka dakatar da shi, ka bashi shawara, da yayi hakuri ya cigaba da harkokinsa, har zuwa lokacin da Allah zai kawo masa mafita.
Rayuwa dai ɗaya ce.
Kar ka jefa ta cikin hadari saboda maganar wanda ya san ribarsa, ba rayuwarka ba.
A Kiyaye!
Allah Ubangiji Yasa Mu Dace Amin.
Daga Usman Tijjani Rijiyarlemo
More from TimesPosts

Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta bayyana cewa har yanzu ba ta iya tantance ainihin inda Iran ta ajiye wasu muhimman kayayyakin ura
Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta bayyana cewa har yanzu ba ta iya tantance ainihin inda Iran ta ajiye wasu muhimman kayayyakin uranium da aka inganta (Enriched Uranium) ba,…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya Na Gabashin Duniya :: Shin Mai Yake Shirin Faruwa.Sun yi da dare , sun fitar da mumunar gargadi
Sun yi da dare , sun fitar da mummunar gargadi Iran ta fitar da sabbin gargadi ga rundunar Amurka ta jiragen yaƙin marasa matuƙa na Scorpion Strike, inda ta ce tana sa ido kan sansanoninsu da wuraren…
Ay Abdullahi1 min read

Shin Ko Kunsan kuwa Wane Irin mataki American Da Israel Suke shirin Daukewa, akan Iran , San Ita Kuma Iran Wane Irin Shiri Tayi
Tun da kaga manyan hukumomin leƙen asirin America da Isra’ila musamman (CIA da MOSSAD) sun masa gano takamaiman inda Iran take ajiye da Enriched Uranium ɗin ta a duniya, Allah ina maka rantsuwa da…
Ay Abdullahi2 min read