Obama ya bukaci yan jam'iyyar Democrat su yi amfani da nasarar zabukan su wajen kawo sauyi a Amurka
Obama ya bukaci yan jam'iyyar Democrat su yi amfani da nasarar zabukan su wajen kawo sauyi a Amurka Tsohon shugaban kasar Amurka Barack obama ya bukaci yan jam’iyyar Democrat da suyi amfani da ikon…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Obama ya bukaci yan jam'iyyar Democrat su yi amfani da nasarar zabukan su wajen kawo sauyi a Amurka
Tsohon shugaban kasar Amurka Barack obama ya bukaci yan jam’iyyar Democrat da suyi amfani da ikon da suka samu a majalisar dokokin Amurka wajen kawo sauye-sauye domin samun kyakkyawan makoma ga kasar.
Jam’iyyar Democrat ta samu gagarumar nasara a zaɓen tsakiyar zangon mulki da aka gudanar ranar Talata, inda ta ƙwace cikakken iko da Majalisar Dokokin Amurka daga hannun jam’iyyar Republican ta Shugaba Donald Trump.
Obama ya bayyana nasarar a matsayin saƙo karara daga al’ummar Amurka, yana mai cewa jama’a na son shugabannin da za su haɗa kan mutane maimakon rarrabasu, tare da samar da mafita ga matsalolin da su ke fuskanta.
Ya ce duk da cewa gwamnatin Trump tana da sauran shekaru biyu a kan mulki, ya kamata ’yan Democrat su tashi tsaye, su yi amfani da damar da suka samu wajen kawo sauye-sauye da hana ƙarin lalacewar al’amura.
A nasa ɓangaren, Shugaba Donald Trump ya bayyana rashin jin daɗinsa kan sakamakon zaɓen, inda ya yi iƙirarin cewa da a ce yana takara, da jam’iyyarsa ta samu gagarumar nasara.
More from TimesPosts

Labaran Siyasa :: Na taɓa zama direban tasi dan kawai na biya wa kaina kuɗin makaranta - Tinubu
Na taɓa zama direban tasi dan kawai na biya wa kaina kuɗin makaranta - Tinubu Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya taɓa yin aikin tuƙin taxi da wasu ayyuka daban-daban a ƙasar Amurka…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran siyasa. ::: INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027
INEC za ta yanke hukunci kan makomar Pantami da Gwarzo a zaɓen 2027Hukumar zaɓe mai zaman Kanta ta kasa (INEC) za ta yanke hukunci kan ƙorafe-ƙorafen wasu ‘yan takarar gwamna da aka cire sunayensu…
Ay Abdullahi1 min read

Ɗan majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi iƙirarin cewa albashin sabon ma’aikacin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya ninka nasa sau 3
Ɗan majalisar wakilan Najeriya, Alhassan Ado-Doguwa, ya yi iƙirarin cewa albashin sabon ma’aikacin Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur ta Najeriya (NUPRC) ya ninka nasa sau 3.Doguwa, wanda ke…
Ay Abdullahi1 min read