Skip to content
TimesPosts homeTimesPostsThe record, as it happens.

Shin Ko Kunsan kuwa Wane Irin mataki American Da Israel Suke shirin Daukewa, akan Iran , San Ita Kuma Iran Wane Irin Shiri Tayi

Tun da kaga manyan hukumomin leƙen asirin America da Isra’ila musamman (CIA da MOSSAD) sun masa gano takamaiman inda Iran take ajiye da Enriched Uranium ɗin ta a duniya, Allah ina maka rantsuwa da…

Ay Abdullahi · Admin

· 2 min read

Tun da kaga manyan hukumomin leƙen asirin America da Isra’ila musamman (CIA da MOSSAD) sun masa gano takamaiman inda Iran take ajiye da Enriched Uranium ɗin ta a duniya, Allah ina maka rantsuwa da Allah ba wata ƙungiya ko wani mutum a duniya da ya isa ya bayyana maka ƙarfin ikon da Iran take da shi yanzu a duniya. Duk wannan harbe-harben da rushe-rushen da America da Isra’ila suka yi tayi a lokacin yaqin nan da Iran ashe duk ƙarya ce lalube ne kawai su ke yi cikin duhu 'ya'yan asara 😀. Har yanzu ba su ma san inda “enriched nuclear material” ɗin Iran yake ba har yanzu. Ka dai duba ƙarfin leƙen sirri irin na hukumomin CIA da MOSSAD da kuma irin maƙudan biliyoyin dalolin da su ka kashe tsawon watanni suna neman inda Nuclear Facilities ɗin Iran suke, amma wlh har yau ɗin nan sun kasa gano exact facilities ɗin. Kuma abinda zai sake baku mamaki, har yau ɗin nan sun kasa gano inda Supreme Leader Mojtaba Khomeini yake.

Bawai iya location ɗin da exact Nuclear Facilities ɗin Iran ɗin bama suke, Malam hatta mutanen da suke da alaƙa da Nuclear Facilities ɗin ma basu sani ba 'yan wahala. Duk boma-boman da America da Isra'ila suka yi ta harbawa zuwa Iran wlh duk akan empty mountains suka yi ta harbawa. Ashe duk lalube ne cikin dubu suke ta yi 'ya'yan asara. Idan kana ganin yadda America take magana akan nuclear ɗin Iran a gidajen TV da Radio kai sai ka rantse da Allah cewa kamar gashi nan a tafin hannun su suna kallon komai kawai kamar basu ga damar lalata shi bane😀👌. Yanzu dake sun gama casawa sun ga babu tsaba, yanzu kuma sun saka bounty na zunzurutun kuɗi kimanin 27 Billion Naira cewa duk wanda yazo da cikakken information ɗin wurin da Iran take sarrafa makamin Nuclear ɗin ta zasu bashi wannan kuɗin take-yanke. Sun gama yin duk abinda zasu yi a kan Iran dole sun ga uwar-bari sun koma bounty competition. Malam Iran ta gama wahalar da mutanen nan. Matuƙar aka ce shugabannin ƙasar ka karnuka ne marasa albarka wlh har abada kun yi hannun riga da kima a idon duniya. Iran kaɗai ta ishe ka misali 🫂👌.

©Salisu Yakubu

More from TimesPosts

Shin Ko Kunsan kuwa Wane Irin mataki American Da Israel Suke shirin Daukewa, akan Iran , San Ita Kuma Iran Wane Irin Shiri Tayi | TimesPosts